Shafin Farko Sashin Blog Hanyar Tuntuba

Alhausawiy » Blog » RABBUNALLAH RABBUNALLAH KAI SALATI GUN MA AIKI

RABBUNALLAH RABBUNALLAH KAI SALATI GUN MA AIKI

Wallafan December 9, 2020. 5:17pm. Na Mustapha Aminu Rabiu. A Sashin Mustaphal Ameen Alhausawiy
Fari nasa wanda yai dukkanin halitta Jalla sarki.
Kai dubun tsira aminci ya Ilahi gun maaiki.
Sa sahabbai da Alihi har shurafa u masu tsarki.
Jiyali bahrul ulumi uhayyika jikan maaiki.
Yafikowa isa da girma ba yamanzo batu natsarki.
Shiyazam mai kadaita Allah tun gabanin masu Tsarki.
Ya wuce dukkan hijabai yaga Allahu bamafarki.
Bayashi sammai da Qassai ga sonsa wallah naketadoki.
Wahwa hablullahi dangi baamo to bare tatsinke.
Gwadaben shiriya kusan sansanin haya une Maaiki.
Shiyazam haskennawahi garkuwar Qudubai maaiki.
Dahane hujjar maaika dashi sukai koyi aaiki.
Yafi jibrilu yafimikalu Rabbi shine yabashi tsarki.
Yafi Adam Isa khalilu Jalla shine yabashi tsarki.
Kai mumike mugaida manzo 'yan uwana mukyauta Aiki.
Wanda yassoshi ya rabauta anan da can baishiga hayaQi.
Maifadi mai zayacema kafi Qaulin masu baki.
Ni Ina kaunarka Yasin kasoni dominna samu tsarki.
Nadina birnin Isa da girma garin mazo Aiki nakirki.
Wanda yasso madina dangi kuce Ina sonsa so nakirki.
Kubarni dangi Intai madina aQafa koko kubani doki.
Manzamo mai kudi dazan hau Erofilen Inzo gareki.
Dala shauQi fiki ya daibatu yaushe zanaganki.
Anbatonki kesan nishadi kice ina gaida maaiki.
Ya hawa dauki duk batuna kikaiwa sarkin masu Tsarki.
Ya Rasulallah kayarda nazo nagaisheka ya Maaiki.
Dan isar fatima batula da mijinta Aliyyu zaki.
Dan Abubakari da Umar da Uthman da Jafar sadauki.
Dan Hassan dan Hussaini muhsin Umama Zainab ya maaiki.
Dan jamiul Ashabi da Alihinka masu tsarki.
Rabbana kajji Qanmahaifan malamina Aliyyu zaki.
Mustapha da gun Aminu ke fadin Assalam dakirki

Tura wannan zuwa:

Game da Mawallafi:

Babu hoto
Mustapha Aminu Rabiu
Sunana Mustapha Aminu Rabiu wanda akafi sani da Alhausawiy Dake garin Kano a Najeriya karamar hukumar Gwale a unguwa da ake kira da Hausawa gida mai lamba 199

Taken Muhimmin Sako

Muhimmin sakon shafin zai kasance a nan...

Kasidu Masu Alaka